Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yaba tare da alfahari da irin kyawun sura da Allah ya yiwa matar dansa. Fasoye ya ba amaryar tabbacin cewa dansa ba zai ci amanarta ba saboda tana da kyau, shafaffen tumbi da kuma fararen hakora Fayose ya yi magana ne a cikin wani bidiyon bikin wanda ya bayyana kuma ya shahara a ranar Talata. A cikin bidiyon, yayin da yake bayar da jawabin uban ango, wanda yake wajibi bisa al'adar Yarbawa, Fayose ya ce kyawun mace yana taka muhimmiyar rawar gani wajen daidaita aure. Ya kuma ce mazajen da basu da kyawawan mata "suna karewa da cin amanar aurensu", jaridar The Cable ta rahoto.
Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Awaren Biafra Da Cafke Daya Dakarun da ke gudanar da Atisayen GOLDEN DAWN sun sami nasarar hallaka wani Kasurgumin ɗan ƙungiyar ‘yan awaren Biafra bayan ya kai hari a sansanin rundunar da ke Amaekpu da ke ƙaramar hukumar Ohafia a jihar Abia ranar Alhamis da ta gabata. Rundunar ta bayyana wannan nasarar da ta samu ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar ran Alhamis mai ɗauke da sa hannun Birgediya Janar Onyema Nwachukwu wanda shi ne daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Nigeriya. A cewar rundunar, “Maharan waɗanda ke ɗauke da makamai a cikin motoci sun buɗe wuta kan sansanin dakarun, inda suka fuskanci turjiya aka kuma murƙushe ɗaya daga cikin su. Bayan sauran Maharan sun tsere, dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar harba ruga. “Bayan ‘yan ta’addan sun tsere a sakamakon shan kashi ne, dakarun sansanin Ohaozara da ke jihar Ebonyi suka cafke su a Eda, inda suka ƙwace motoci uku da kame dan bindiga ɗaya.
The RED state are at high risk of lightning 🌩️, thunderstom and flood attack. Be prepared and stay alert for the aftermath, south-south. South-east. North-east. North-central will the region to experience more intense of lightning. If you here thunderstorm find the shelter and be safe
Comments
Post a Comment