Daga shamsuddeen. Jaruma Mansurah Isah ta yi wani rubutu a kan tsohon mijinta, Sani Musa Danja, tare da sakin wasu sabbin hotunanta tare da shiJarumar ta nuna cewa tana da kyakkyawar alaƙa tsakaninta da shi, kuma ta yi wasu kalamai na barkwanci akan JaruminTuni dai masoyan ta suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan sabon rubutun, inda mafi yawa suke rokonta da su sasanta kan su ga abinda Jarumar ta wallafa a shafinta na instagram ''Ya kamata na sassauta mishi, Jaruma Mansurah Isa ta sake magana kan tsohon mijinta Sani Danja Hoto: @Mansurah_Isah Sannan takara dacewa, ''"Eyyah, Ɗan bawan Allah, shin murmushi yake yi kuwa? ku taimaka ku taya ni dibawa dan allah.""Bai kamata wanna kwalliya ta tafi a banza ba, ina tunanin ya dace in sassauta masa na buɗe shi ko zai ga wannan rubutun." To dama ai hausawa sunce da tsohuwar Zuma ake magani.