Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon general manager na hukumar tashar jiragen ruwa a kano
Anyi garkuwa da tsohon general manager na hukumar kula da tashohshin jiragen ruwa ta kasa Bashir M Abdullahi a Kano.
Anyi garkuwa da shi ne a yammacin yau laraba a gonarsa da ke kauyen Gomo a karamar hukunar Sumaila.
Wani mazaunin kauyen na Gomo ya ce wasu Yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba ne su kai awon gaba da shi a yayin da yake duba gonarsa da ke kauyen.
Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa ba shi da masaniya a kan lamarin, amma zai bincika ya sanar da hakikanin lamarin.
Comments
Post a Comment