Dana ba zai ci amanarki ba saboda kina da kyau – Tsohon gwamna ga surukarsa
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yaba tare da alfahari da irin kyawun sura da Allah ya yiwa matar dansa. Fasoye ya ba amaryar tabbacin cewa dansa ba zai ci amanarta ba saboda tana da kyau, shafaffen tumbi da kuma fararen hakora Fayose ya yi magana ne a cikin wani bidiyon bikin wanda ya bayyana kuma ya shahara a ranar Talata. A cikin bidiyon, yayin da yake bayar da jawabin uban ango, wanda yake wajibi bisa al'adar Yarbawa, Fayose ya ce kyawun mace yana taka muhimmiyar rawar gani wajen daidaita aure. Ya kuma ce mazajen da basu da kyawawan mata "suna karewa da cin amanar aurensu", jaridar The Cable ta rahoto.
Comments
Post a Comment